ABNA24 : Shugaban kasar ta Iran ya ci gaba da cewa; Muna taya ku murna saboda karbar jagorancin kasar Kuwaiti wacce kawa ce kuma ‘yar’uwa ga Iran.
A ranar Larabar da ta gabata ne dai sabon sarkin na Kuwaiti Nawwaf al-Ahmad, al-Sabah ya yi rantsuwar kama aiki a gaban majalisar kasar a matsayin wanda ya gaji sabah al-Ahamd, al-sabah, wanda ya rasu a ranar 29 ga watan Satumba da ya shude.
Tun da fari, ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jadaw Zarif ya kai ziyarar aiki kasar ta Kuwaiti a jiya Lahadi, inda ya gana da sabon sarkin.
342/